14 Disamba 2019 - 04:40
An Dauki Tsauraran Matakan Tsaro A Ya yin Gudanar Da Zabuka A Kasar Algeria

Da safiyar yau alhamis 12 ga watan Disamba ne aka bude rumfunan zabe a fadin kasar Algeria domin gudanar da zaben shugaban kasa da ke ciki da ruddani, tun bayan da aka tilastawa tsohon shugaban kasar Abdul Aziz Boutefilika sauka daga kan mukaminsa a farkon wannan shekarar.

(ABNA24.com) Da safiyar yau alhamis 12 ga watan Disamba ne aka bude rumfunan zabe a fadin kasar Algeria domin gudanar da zaben shugaban kasa da ke ciki da ruddani, tun bayan da aka tilastawa tsohon shugaban kasar Abdul Aziz Boutefilika sauka daga kan mukaminsa a farkon wannan shekarar.

Sai dai duk da ci gaba da zanga zangar da ake ci gaba da yi na neman a dage lokacin gudanar da zaben, wannan bai hana kwarar mutane zuwa rumfunan zabe domin kada kuri’unsu ba, babar bukatar masu zanga- zangar ita ce dukkan tsoffin mukarraban gwamnatin su koma gefe su bawa matasa masu jinni ajika dama su tsaya takara kafin shirya wani zabe.

Kimanin yan takara 5 ne suke hammaya na neman kujerar shugabancin kasar, in biyu daga cikinsu tsoffin Fira ministoci ne,sauran guda biyun kuma tsoffin mministoci ne, lamarin da yan adawa ke ganin ba ta canza zani ba duk kanwar ja ce, don haka suka bukaci a kauracema zaben

Sai da rahotanni da muka samu sun bayyana cewa jin kadan bayan bude rumfunan zabe a yankunan arewacin kasar wasu mahara sun kwashe akwatunan zabe a wasu mazabun, tare da lalata katunan zabe da ya ga hotunan yan takara a yankin Kabylie inda yan kabilar Barbar suka fi yawa da suke yi kaurin suna wajen nuna adawa da zaben shugaban kasar.



/129